Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, al’adu da dai sauransu…

00:00
00:00

Resumen del episodio

Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun jingine batun ƙara farashin mai duk da cewa Majalisar Dokokin Riƙon Kwaryar ƙasar ta bayar da shawarar yin wannan ƙari don magance ƙaracin makamashi da ake fama da shi a ƙasar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar da wani shirin rage farashin mai a tsawon wata ɗaya domin sauwaƙa wa jama’a. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyin jama'a...

Episodios

777-

Ra'ayoyin masu sauraro kan jingine shirin ƙara kuɗin mai a Nijar

Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun jingine batun ƙara farashin mai duk da cewa Majalisar Dokokin Riƙon Kwaryar ƙasar ta bayar da shawarar yin wannan ƙari don magance ƙaracin makamashi da ake fama da shi a ƙasar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar da wani shirin rage farashin mai a tsawon wata ɗaya domin sauwaƙa wa jama’a. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyin jama'a...

12 oct. 2026
776-

Ra'ayoyin masu saurare kan kawo ƙarshen wasa da Argentina da Messi yayi

Ra'ayoyin masu saurare kan wasan ƙarshe da Ɗan wasa Lionel Messi ya bugawa ƙasarsa. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Kabiru Muhammad Dan Bauchi.

08 oct. 2026
775-

Ra'ayoyin masu saurare kan fatan ci gaba da haƙo man fetur a wasu sassan arewacin Najeriya

Taron gwamnonin jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya da ya gudana a ƙarshen mako, ya buƙaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gaggauta farfaɗo da aikin binciken man fetur da aka faro tsawon shekaru a yankin. Kazalika taron ya buƙaci gwamnatin da ta mayar da hankali wajen gyara layin dogon da ya haɗa biranen Port-court-Jos-Bauchi-Gombe zuwa Maiduguri saboda muhimmancinsa wajen buƙasa tattalin arzikin al’ummar yankin. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

06 oct. 2026
774-

Ra'ayoyin masu sauraro kan ƙarancin makamashi a wasu ƙasashen yammacin Afrika

Yayin da kusan a kowane mako ana iya a wayi gari da sabon farashin man fetur a Najeriya, a Jamhuriyar Nijar ana fama da ƙaranci da kuma tsadarsa ne a wasu jihohin ƙasar, yayin da ake fama da gagarumar matsalar ƙarancin gaz da ake amfani da shi domin girki. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

29 sep. 2026
773-

Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta

Yau juma'a kamar yadda aka saba, sashen Hausa na RFI na bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan dake ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga siyasa, tattalin arziƙi, tsaro, zamantakewa da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

18 sep. 2026