Wasanni

Wasanni

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

00:00
00:00

Resumen del episodio

Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan mako, zai dubu ne kan bankwanan da Lionel Messi ya yi da tawagar Argentina. A farkon watan Oktoban nan da muke ciki ne kyaftin ɗin tawagar ƙasar Argentina Lionel Messi, yayi bankwana da tawagar bayan kwashe tsawon shekaru 21 tana wakiltar ƙasar a wasannin matakin ƙasa da ƙasa. Messi ya fara bugawa Argentina wasanni ne a ranar 17 ga watan Agustan shekarar 2005 a wani wasan sada zumunci da suka yi da Hungry, inda ya samu nasarar buga wasanni 208, kafin murabus ɗinsa a ƙarawarsu da Benin a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2026. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..

Episodios

683-

Messi ya yi bankwana da tawagar Argentina bayan doka wasanni 208

Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan mako, zai dubu ne kan bankwanan da Lionel Messi ya yi da tawagar Argentina. A farkon watan Oktoban nan da muke ciki ne kyaftin ɗin tawagar ƙasar Argentina Lionel Messi, yayi bankwana da tawagar bayan kwashe tsawon shekaru 21 tana wakiltar ƙasar a wasannin matakin ƙasa da ƙasa. Messi ya fara bugawa Argentina wasanni ne a ranar 17 ga watan Agustan shekarar 2005 a wani wasan sada zumunci da suka yi da Hungry, inda ya samu nasarar buga wasanni 208, kafin murabus ɗinsa a ƙarawarsu da Benin a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2026. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..

12 oct. 2026
682-

Yadda ƴan wasa ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin hutu

Shirin a wannan mako ya yi duba ne kan yadda ƴan wasan da ke taka leda ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin da suke hutu. A duk lokacin da aka kammala wasannin lig-lig a kan tafi hutu a kowace shekara musamman a nahiyar Turai da lig ɗin su ya fi jan hankali, wanda hakan kuma ke buɗe wani babi na wasanni a yankuna daban-daban da ƴan wasan ke fitowa domin nuna bajintarsu a zahiri a wasannin sada zumunta da a ke shirya musu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

05 oct. 2026
681-

An kammala gasar tseren Keke ta ƙasa karo na 6 a Jamhuriyyar Nijar

Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda aka gudanar da gasar tseren keke a jihar Maradi da ke Jamhuriyar Nijar. Wannan ne dai karo na 6 da ake gudanar da gasar da ta haɗa masu wannan wasa daga jihohi 8 na ƙasar, da nufin samun gwarazan shekara sannan kuma a zaɓa ƴan wasan da za su rinƙa wakiltar ƙasar a gasanni daban daban kama daga nahiyar Afirka dama matakin duniya idan dama ta samu. Ku latsa alamar sauto don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...............

28 sep. 2026
680-

Duniyar Wasanni: Wace waina ake toyawa a gasar Frimiya Lig ta Ingila

Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda al’amura ke gudana a gasar Firimiya lig ta Ingila. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh

21 sep. 2026
679-

Ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a matakin Unguwanni sun fara cinikayyar ƴan wasa

Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda ake cinikayyar ƴan wasa a matakin ƙananan ƙungiyoyin Unguwanni. A yanzu dai ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da ke buga wasanni a matakin Unguwanni a jihar Kaduna, tuni suka rungumi tsarin cinikayyar ƴan wasa domin ƙarawa ƙungiyoyinsu ƙarfi. Wasu daga cikin masu horas da irin waɗannan ƙungiyoyi sun ce wannan tsarin cinikayya ya taimaka wajen kawo ƙarshen rigingimu da a ke samu kan ƴan wasa, sannan kuma ana gudanar da ita ne kan kuɗin da suka fara daga naira dubu 30 zuwa sama. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............

07 sep. 2026